Mali : An Kashe Sojojin MDD Biyu A Kidal
-
wata mota MDD mai sulke a Mali
Ko a makon daya gabata ma a kai wani hari makamancin wannan a arewacin kasar ta Mali
Rahotanni dake fitowa daga Mali na cewa sojojin MDD biyu ne suka rasa rayukan su a wani hari da wasu masu kaifin kishin addini suka kai a sansanin tawagar Munusma dake Kidal a arewacin kasar.
kamar yadda wata majiya tsaro ta shaidawa a tawagar ta shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP ta ce an kai harin ne da sanyin safiyar wannan juma'a inda kuma wasu sojoji 30 suka raunana wanda cikin su 7 na cikin mawuyacin hali..
wannan harin dai na zuwa ne mako guda kacal bayan wani makamacinsa da kungiyar Al'Qaida reshen kasashen larabawa wato AQMI ta kai kan tawagar 'yan sanda na MUNUSMA dake wani tsohon hotel a birnin Tombuktu da yayi sanadin mutuwar sojan Mali guda.