Wasu Mutane Dauke Da Makamai Sun Kashe Sojojin Mali A Arewacin Kasar
Majiyar Jami'an tsaro kasar Mali daga arewacin kasar ta bayyana cewa wasu yan bindiga sun kashe sojoji ukku a kusa da birnin Timbuktu babban birni a arewacin kasar.
Majiyar Jami'an tsaro kasar Mali daga arewacin kasar ta bayyana cewa wasu yan bindiga sun kashe sojoji ukku a kusa da birnin Timbuktu babban birni a arewacin kasar.
Jaridar Lefigaro ta kasar Faransa ta nakalto labarin cewa a yau jumma'a wasu yan bindiga a garin Goundam mai tazarar kilomita 90 daga birnin Timbuktu sun kashe sojojin kasar Mali ukku wadanda suke cikin wata mota a yankin.
Majiyar bata bayyana wace kungiya ce daga cikin kungiyoyin da ke dauke da makami a yankin ne da aikata kissan ba. A cikin yan kwanakin nan dai kungiyar almurabitoon wacce take biyayya ga kungiyar al-qaeda ta dauki alhakin kai wasu hare hare a wurare da dama a kasar Mali da kuma Borkina Faso.