Matsanancin wuyar Ruwa a kasar Afirka ta Kudu
Rashin Saukar Ruwan Sama ya janyo matsanancin Wuyar Ruwa a kasar Afirka ta kudu
Rahotanni dake fitowa daga kasar Afirka ta Kudu na cewa ruwa da aka tare da manya-manyan madatsar ruwan kasar ya ragu, kuma an samu karamcin saukar ruwan sama a shekarar bara, wanda hakan shi ya janyo karamcin ruwan sha da Al'ummar kasar ke fama da shi a halin da ake ciki.
Rahoton ya ce ya zuwa yanzu Gwamnati ta kashe tsabar kudi har dalar Amurka million 32 domin kai ruwa a yankunan da ba su da ruwa a kasar.
A wata sanarwa da Gwamnatin kasar ta bayar karamcin ruwan sama ya yi sanadiyar raguwar samun albarkatun gona da kashi 14%
A nata bangare hukumar samar da abinci ta Duniya FAO ta ce farin da kasar Afirka ta kudun ta fuskanta a shekarar da ta gabata ya jefa rayuwar mutane million 16 cikin barazana, kuma a kwai yuyuwar adadin ya karu zuwa million 50.