Shugabancin Kungiyar Afirka: Uganda ta bukaci Goyon Bayan Kasar Aljeriya
(last modified Fri, 17 Jun 2016 06:21:14 GMT )
Jun 17, 2016 06:21 UTC
  • Shugabancin  Kungiyar Afirka: Uganda ta bukaci Goyon Bayan Kasar Aljeriya

An yi tattaunawa a tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen uganda da Aljeriya Akan Tarayyar Afirka.

Ministan harkokin wajen kasar Uganda Henry Oryem Okello, wanda ya gana da takwaransa na Aljeriya, Ramdhan Lamamra a birnin Ages , ya bukaci samun goyon bayan Aljeriya akan shugabantar kungiyar Tarayyar Afirka.

Okello ya ce; Muhimmancin da matsayin ya ke da shi ne ya sa ya zama wajibi a gudanar da sauye-sauye sannan kuma da kwararrun da za su tafiyar da shi, domin bayyana yadda Afirka ta ke a duniya.

A ranakun 17 zuwa 18 ga watan Yuni ne za a yi taron kungiyar tarayyar Afirka a kasar Ugandan da za a tattauna batun wanda zai maye gurbin Nkosazana Dlamini Zuma mai rike da shugabncin kungiyar a yanzu.