Gwamnatin Nijar Ta Musanta Batun Tura Sojojin Chad Yankin Diffa
(last modified Sun, 19 Jun 2016 11:02:20 GMT )
Jun 19, 2016 11:02 UTC
  • Gwamnatin Nijar Ta Musanta Batun Tura Sojojin Chad Yankin Diffa

Ministan cikin gidan kasar Nijar Bazoum Mohamed ya bayyana cewar babu wani sojan kasar Chadi da aka tura yankin Diffa da ke kudu maso gabashin kasar da nufin fada da 'yan kungiyar Boko Haram bayan wasu munanan hare-haren da suka kai yanki makonni biyun da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo minista Bazoum Muhammad yana musanta batun tura dubban sojojin Chadi zuwa yankin na Diffa inda ya ce hakan wani labari ne kawai na 'yan jarida. Ministan ya kara da cewa sojojin na Chadi dai suna Nijeriya ne ba su shigo Nijar ba.

A ranar 3 ga watan Yunin nan ne dai 'yan Boko Haram din suka kai wani mummanan hari yankin na Diffa inda suka kashe wasu sojojin Nijar kusan Talatin lamarin da ya sanya shugaban kasar Muhammad Issofou tafiya kasar Chadi don tattaunawa da takwararsa na kasar Idris Derby lamarin da Minista Bazoum din ya ce an yi hakan ne don gaggauta aiwatar da shirin hadin gwiwa na sojoji tsakanin kasashen yankin da nufin fada da kungiyar Boko Haram.

Wasu rahotanni daga kasar Nijar din dai sun ce tuni kasar Chadin ta tura sojojinta zuwa cikin Nijar din da nufin fada da kungiyar ta Boko Haram.