Mali : Kungiyar Ansaruddin Ta Dauki Alhakin Kai Hari Kan Dakarun MDD
Feb 13, 2016 07:49 UTC
-
wani sojin Munusma a Mali
Harin dai na jiya Juma'a yayi sanadin mutuwar sojojin MDD da dama
kungiyar Ansar Dine mai kaifin kishin addini a Mali ta dauki alhakin kai hari kan dakarun MDD a arewacin kasar.
A sanarwar da kungiyar ta fitar ta hanyar kanfanin dilancin labaren Al-Akhbar na Moritaniya, kungiyar ta ce ta kai harin ne da wata mota shake da boma bobai a sansanin sojojin na Kandi dake tsakiyar Kidal, lamarin da yayi sanadin mutuwar sojojin MDD da dama tare da raunana wani adadi mai yawa a harin na jiyya Juma'a.
Sansanin dai na Kidal ya kunshi sojojin Faransa dana tawagar MDD a Mali wato Munusma.
Tags