An Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Matasan Afirka Ta Yamma A Senegal
(last modified Tue, 21 Jun 2016 16:17:35 GMT )
Jun 21, 2016 16:17 UTC
  • An Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Matasan Afirka Ta Yamma A Senegal

An gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta matasan kasashen Afirka ta yamma karo na ashirin da hudu a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labaran Pars Today ya nakalto daga shafin cibiyar yada al'adun muslunci ta jamhuriyar musulunci ta Iran cewa, shugaban ofishin yada al'adun muslunci na Iran a kasar Senegal Sayyid Hassan Ismati shi ne ya jagoranci taron rufe gasar, tare da halartar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar Senegal.

Gasar dai ta samu halartar matasa makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki daga wasu daga cikin kasashen yammacin Afirka da suka hada da ita kanta kasar ta Senegal da Mauritaniya, Mali, Gambia da sauransu, kamar yadda kuma wasu daga cikin manyan malaman addini musamman na darikar Tijjaniya da wasu darikokin sufaye na kasar da kuma wasu 'yan siyasa sun halarci wurin.

Shugaban ofishin yada al'adun muslunci na kasar Iran a Senegal Sayyid Hassan Ismati ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya bayyana cewa kur'ani mai tsarki da sunnar manzon Allah su ne za su hada musulmi baki daya a wuri guda duk kuwa da irin banbancin fahimta kan wasu mas'aloli da ke tsakaninsu, amma wadannan manyan abubuwa biyu kur'ani da sunnar ma'aiki sun hada su.

Daga cikin wadanda agayyata domin yin alkalanci a wurin wannan gasa, akwai baki daga kasashen Libya, Kuwait, Saudiyyah, Iran, da kuma Masar, a karshen taron an bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a bangarorin gasar.