Senegal : Shugaba Macky Sall, Yayi Wa Karim Wade Ahuwa
Rahotanni daga Senegal na cewa shugaban kasar Macky Sall, yayi wa Karim Wade dan tsohon shugaban kasar Abdulaye Wade Ahuwa.
A bara ne dai wata kotun Senegal ta yankewa karim Wade daurin shekaru shida gidan yari da tarar sama da dala miliyan dari biyu, saboda samunsa da laifin azurta kansa ta hanyar da bata dace ba a zamanin mulkin mahaifinsa.
ko baya ga Karin Wade akwai wasu mutane biyu dake da irin wannan laifin wadanda suka hada da Ibrahima Abou Khalil da Alioune Samba Diassé da wannan matakin ya shafa, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta sanar.
Saidai a cewar sanarwar matakin na saki ne kawai, bai shafi tara da kuma kudaden da masu laifin zasu mayar ba.
Dama kafin hakan rahotanni daga kasar sun rawaito inda shugaban Macky Sall ke gayawa wata tawagar mayan maluman addini na kasar cewa, da yardar Allah Karim Wade zai yi karamar Sallah a cikin iyalinsa.
Karim Wade dai shi ne jam'iyyar adawa ta kasar ta zaba a matsayin dan takararta na shugaban kasa.