An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasa A Uganda
An fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a karo na huku a kasar Uganda wanda gidan talabijin na gwamnatin kasar UBC ke watsawa kai tsaye.
Kamfanin dillancin labaran kasar Iran ya bayar da rahoton cewa, ofishin kula da harkokin ilimi da al'adu na jamhuriyar mulsunci ta Iran ya dauki nauyin shirya wannan gasa ta kur'ani mai tsarki a kasar ta Uganda, tare da halartar Ali Bakhtiyari shugaban ofishin yada al'adu na jamhuriyar mulsunci ta Iran a kasar, sai kuma Ronald Kayizi shugaban hukumar ratalabijin ta UBC ta kasar, da Haji Abdul Nsurku, da Rafsanjani Tatiya bababn daraktan kula da watsa shirin talabijin ta kasa, sai kuma wasu manyan jami'ai an jami'oin kasar, da sauran makaranta da mahardata daga sassa na kasar.
Wannan shi ne karo na hud da ake gudanar da wannan gasar kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya akasar ta Uganda, wadda jamhuriyar musulunci ta Iran ke daukar nauyin shirya da kuma gudanarwa, inda daruruwan musulmi daga sassa na kasar suke halartar, baya ga makaranta da mahardata kur'ani da ke halartar gasar, malaman addinin muslunci na kasar ma suna a sahun gaba wajen bayar da gudunmawarsu domin ganin shirin ya yi nasara.
Ronald Kayizi shugaban hukumar talabijin ta kasar UBC ya fadi a wurin bude taron cewa, suna farin ciki matuka dangane da wannan kokari da ake yi na shirya gasar kur'ani a kasarsu, wanda hakan zai ba musulmi 'yan kasar Uganda damar gudanar da wani babban taro nasu wanda talabijin na kasa zai watsa kai tsaye.
Shi ma a nasa bangaren shugaban ofishin raya al'adu na jamhuriyar muslunci a kasar Ali Bakhtiyari ya gabatar da nasa jawabin, inda ya ce ko shakka babbu kur'ani mai tsarki da sunnar manzon Allah (SAW) su ne muhimman abubuwan da suka hada musulmi, kuma idan musulmi suka yi riko da su, da kuma yin aiki da koyarwarsu, to za su samu shawo akn matsaloli da dama da suke ci musu tuwo a kwarya.
Daga karshe ya yi kira ga dukkanin musulmin kasar ta Uganda da su ci gaba da zama abin buga misali da su wajen hadin kan musulmi, ganin yadda suke haduwa suna gudanar da tarukan addini ba tare da nuna wani banbancin fahimta da ke tsakaninsu ba.