Fada tsakanin Mazauna kauyuka biyu a kasar Mali.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7255-fada_tsakanin_mazauna_kauyuka_biyu_a_kasar_mali.
Fada tsakanin Mazauna kauyuka biyu ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T06:58:30+00:00 )
Jun 26, 2016 07:31 UTC
  • Fada tsakanin Mazauna kauyuka biyu a kasar Mali.

Fada tsakanin Mazauna kauyuka biyu ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasar Mali.

Majiyar Gwamnatin kasar Mali ta sanar da aukuwar fada tsakanin mazauna kauyukan Mouya da Koussouma dake yankin Mopti, lamarin da yayi sanadiyar asarar rayuka 14 yayin da da wasu 42 na daban suka jikkata.

Rahoton ya ce tuni aka tura Dakarun tsaro yankin domin dawo da doka da oda.

A cewar Gwamnan jihar ta Mopti, babban abinda Gwamnati ta sanya a gaba shine dawo da konciyar hankali a wadannan kauyuka.

Ana sa ran a wannan Lahadi Gwamnatin jihar ta Mopti zai ziyarci gurun aukuwar tashin hankalin.

Rikici tsakanin mazaunan kauyukan ya samo asali ne tun a shekaru da dama kuma lamari ya kasance a kan gardama na wasu filayen Noma.