Sojojin Faransa Sun fara kai wani sabon farmaki a Arewacin Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7360-sojojin_faransa_sun_fara_kai_wani_sabon_farmaki_a_arewacin_kasar_mali
Majiyar Tsaron kasar Faransa ta sanar da fara kai wani sabon farmaki a arewacin kasar Mali
(last modified 2018-08-22T06:58:30+00:00 )
Jun 28, 2016 06:51 UTC
  • Sojojin Faransa Sun fara kai wani  sabon farmaki a Arewacin Kasar Mali

Majiyar Tsaron kasar Faransa ta sanar da fara kai wani sabon farmaki a arewacin kasar Mali

Majiyar ta bayyana cewa farmakin da aka bashin lakabin Barkhane, an fara shi ne da nufin yakar kungiyiyoyin ta'addanci da kuma masu safarar makamai gami da miyagun kwayoyi.

Farmakin da ya fara a jihohin Kidal da Gao dake arewacin kasar, ya zuwa yanzu, Sojojin Faransa sun sanar da tsare mutane 4 da ake zarki mayakan kungiyoyin dake dauke da makami ne da kuma kayan aikin Soja daga ciki har da wata Motar aikin soja.

Majiyar ta ce kafin a meka wadanda ake zarki ga hanun Dakarun tsaron na Mali, sai sun fuskanci tambayoyi daga Sojojin na Faransa., kuma za a ci gaba da kai wannan farmaki har zuwa wasu kwanika masu zuwa kamar yadda majiyar sojin Faransar ta bayyana.

Yankunan Arewacin Malin dai sun fada cikin rikici tun bayan da kungiyoyin dake dauke da makamai suka karbe iko da shi a shekarar 2013.