Majalisar Dinkin Duniya Ta Kara Wa'adin Aikin Dakarunta A Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7426-majalisar_dinkin_duniya_ta_kara_wa'adin_aikin_dakarunta_a_kasar_mali
Majalisar dinkin duniya ta kara wa'adin ayyukan dakarunta masu gudanar da ayyukan wanzar da sulhu da zaman lafiya a kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T06:58:31+00:00 )
Jun 29, 2016 13:05 UTC
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Kara Wa'adin Aikin Dakarunta A Kasar Mali

Majalisar dinkin duniya ta kara wa'adin ayyukan dakarunta masu gudanar da ayyukan wanzar da sulhu da zaman lafiya a kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar a yau, dukaknin mambobin kwamitin 15 sun amince da daftarin kudirin da aka gabatar, da ke neman a kara wa'adin ayyukan dakarun majalisar a kasar Mali.

Kawamitin tsaron ya amince da kara adadin dakaru 2500 domin su hade da takwarorinsu a kasar ta Mali, inda adadin dukkanin dakarun da ke kasar ta Mali zai karu zuwa dubu 13 da 289, sai kuma 'yan sanda 1920.

A gobe 30 ga watan Yuni 2016 wa'adin aikin dakarun ke kawo karshe, inda kuma bayan amincewa da kara wa'adin a yau, za su kara wata shekara guda a kasar ta Mali.