Tsawaita Aikin Dakarun MDD A Mali
kwamitin sulhu na MDD ya kara yawan dakarunsa da kuma tsawaita wa'adin aikinsu a kasar Mali, domin ci gata da tabbatar da aikin wanzarda zamen lafiya.
A zamen sa na jiya Laraba kwamitin ya ce ya dau wannan matakin ne domin ci gaba da kare fararen hula da kuma ma'aikatansa dake fuskantar hare-hare mayakan jihadi a arewacin wannan kasar ta Mali.
Kasar Faransa ce dai ta gabatar da wannan bukata wace ta samu amuncewa daga dukkan kasashe 15 mambobin kwamitin.
Kwamitin dai ya dai amunce da tsawaita aikin tawagar ta MINUSMA da shekara guda, da kuma kara yawan dakarun daga 11.240 zuwa 13.289 kwatamcin karin dakaru 2.500
kazalika kwamitin ya amunce kara yawan 'yan sanda sa daga (1.440 zuwa 1.920)
Babban aikin dake gaban tawagar ta MINUSMA a yanzu shi ne taimakawa gwamnatin Mali wajen aiwatar da yarjejeniyar sulhu da aka cimma yau da shekara guda da 'yan tawaye a arewacin kasar da kuma maido da doka-da-oda a arewaci da kuma tsakiyar kasar da shirya zame mai inganci.
Haka kuma an baiwa wannan Tawagar umurnin daukan dukkan matakan da suka domin aiwatar da aikin ta ciki harda daukan matakin ba sani ba sabo.
Ana sa ran kuma wannan kudirin zai bada damar aikewa da wata tawagar turai mai cikaken kwarewa, a cewar jakadan faransa a MDD, François Delattre.
A watan Mayu daya gabata ne gwamnatin Mali da 'yan tawayen arewacin kasar suka cimma yarjejeniyar sulhu wace har yanzu dai take tangal-tangal.
kwamitin sulhu na MDD yayi amfani kuma da wannan damar domin kira ga bangarorin biyu dasu gaggauta aiwatar da yarjejeniyar ta yadda al'ummar kasar zasu mori zamen lafiya da aka cimma.
MDD dai ta ce zata tattaunawa da mahukuntan Mali domin duba mi yake hana ruwa gudu wajen aiwatar da yarjejeniyar.
Kudirin da MDD ta amunce da shi a wannan karo yayi barazanar kakaba takunkumai da suka dana toshe kadarori da kuma hana tafiye-tafiye ga duk wani da zai kawo cikas ko zagon kasa wajen aiwatar da shirin zamen lafiya ko kuma kai hari wa tawagar MINUSMA.
tawagar MINUSMA na fuskantar babban kalubale inda sanadin hare-haren mayakan jihadi tayi hasaran rayukan dakarun ta 27 da kuma jikatar wasu 112 a cikin shekara guda, lamarin da yasa kwamitin tsaro ya bukaci tawagar data kara himma musamen kan samun bayanai da kuma kwarewa.