An Kashe Sojojin Mali 4 A Wani Hari
Rahotanni daga Mali na cewa sojojin kasar hudu ne suka rasa rayukan su kana guda ya jikkata biyo bayan wani hari da aka kai masu a arewacin kasar.
Sojojin dai na gudanar da aiki ne tabbatar da tsaro ne ga ma'aikatan wani kamfanin gine-gine ne na kasar waje dake tsakanin biranen Tunbuctu da kuma Goundam dake arewa maso yammacin kasar a lokacin da aka kai masu wannan farmaki a cewar wata majiyar soji.
Harin wanda ba'a kai ga tantance ko suwa keda al'hakin kaisa ba, da farko dai yayi sanadin mutuwar sojojin kasar ta Mali uku, kafin daga bisa na hudun ya cika a yau Alhamis.
Wata majiyar 'yan sanda ma ta tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP hakan tare da cewa maharan sun kuma arce da wasu motocin sojojin guda biyu.
Wannan dai na zuwa sa'o'i kadan bayan da shugaban kasar ta Mali Ibrahim Bubakar Keita ya nada janar Didier Dacko a matsayin babban hafsan sojin kasar, wanda ya kasance kafin wannan matsayin kwamandan dakarun kasar dake yakar nayakan jihadi dake da alaka da 'yan ta'adan Al-Qaïda a arewacin kasar.