Harin 'yan bindiga a yankunan arewacin Mali
Harin 'yan bindiga a arewacin Mali ya hallaka Mutane Uku
Majiyar tsaron kasar Mali ta sanar da cewa 'yan bindiga sun sake kaddamar da haki a yankunan arewacin kasar inda suka kashe mutane uku sannan kuma suka sanya Motar MDD wuta.
Harin farkon sun kai shi ne a wani ofishin 'yan sanda dake yankin Maneka na arewacin Kasar a daren juma'a inda suka kashe Mutane uku tare da jikkata wani jami'in Jandarma.
A ranarAlkhamis din da ta gabata wasu 'yan bindigar sun kai hari a yankunan arewacin kasar inda suka hallaka mutane 4.
Tun bayan juyin milkin shekarar 2012, kasar ta Mali ta fada cikin rikici ,inda kungiyoyin 'yan tawayen abzunawa tare da masu tsatsauren ra'ayin addini suka mamaye yankunan arewacin kasar, saidai bayan shigar Dakarun tsaron Faransa da Afirka an samu nasarar 'yanto yankunan, amma duk da haka, ana ci gaba da fuskantar hare-hare, lamarin dake lashe rayukan fararen hula da Sojoji a yankin.