Borkina Fasa Ta Aike Da Karin Sojoji Zuwa Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7627-borkina_fasa_ta_aike_da_karin_sojoji_zuwa_kasar_mali
Fiye Da Sojoji Dari Takwas Ne Borkina Faso ta Aike Zuwa Kasar Mali
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 04, 2016 07:51 UTC
  • Borkina Fasa Ta Aike Da Karin Sojoji Zuwa Kasar Mali

Fiye Da Sojoji Dari Takwas Ne Borkina Faso ta Aike Zuwa Kasar Mali

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato cewa; Kasar Borkina Faso ta aike da sojoji 850 zuwa kasar Mali.

Sojojin na Bornika Faso za su shiga karkashin dakarun majalisar dinkin duniya ce ta; (MINUSMA).

Kasashen Borkina Faso da Mali suna da iyaka mai tsawo a tsakaninsu.

A cikin watan Yuni ma kasar ta Borkina Faso ta girke Gendarme 140 a garin Gao da ke arewacin kasar Mali.

A makon da ya shude ne dai kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya tsawaita lokacin aikin dakarun tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali zuwa 2017.