Senegal : Anyi Wa Firsinoni 600 Afuwa Saboda karama Sallah.
Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya sanya hannu a wata dokar yi wa firsinoni 600 da ake tsareda a gidajen yari na kasar daban daban afuwa.
Wannan matakin dai a cewar wata sanarwa daga fadar shugaban kasar dalilin karama Sallah Aid El-fitr ce ta kawo karshen watan azumin Ramadana.
kazalika wata sanarwa da ma'aikatar shari'a kasar ta fitar ta ce Shugaban Macky Sall ya yi afuwa ga firsinoni da suka sabawa doka domin basu wata dama ta gyara halayensu.
Matakin afuwa dai a cewar sanarwar bai shafi masu muggan laifuka ba kamar na kisan kai, hare-hare da kuma safara miyagun kwayoyi ba.
Wannan matakin kuma na zuwa ne a kasa da mako biyu bayan afuwa da shugaban kasar yayi wa Karim Wade dan tsohon shugaban kasar Abdulaye Wade da aka tsare bisa laifin almubazaranci da dukuyar kasa.