ِDakarun Sulhu na MDD guda biyu sun Mutu a kasar Mali
Akalla Sojin MDD biyu ne suka rasu sanadiyar tashin wani makami na igwa a arewacin Mali.
Dakarun tsaro da Sulhu na Majalisar Dinkin Dauniya a kasar Mali sun sanar a wannan Laraba cewa Sojojin su biyu sun rasa rayukansu sannan wani guda na daban ya jikkata sanadiyar tashin makamin Igwa a yayin da suke atisayin soja a birnin Kidal dake arewacin kasar
Sanarwa ba ta yi karin haske ba, kan wadanda hadarin ya ritsa da su ko 'yan wata kasa ne,
Dakarun tsaro na MDD da ake kira MUNUSMA sun ce tuni aka bude bincike domin gano yadda hadari ya auku, kuma tuni a kwai kontar da wanda ya samu rauni a asibiti domin karbar jiya.
Tun a watanni Maris da Avrilu nashekarar 2012 ne kungiyoyin 'yan tawayen abzunawa da na Larabawa masu tsatsaurin ra'ayin addinin musulinci suka mamaye arewacin kasar ta Mali,wanda hakan ya sanya aka kafa Rundunar hadin gwiwa ta MDD da aka bata lakabin MUNUSMA, kuma daga wancan lokacin zuwa yanzu Dakarun ke jibke a arewacin Mali.