Bincike kan yanayin da kasar Mali ke ciki
Manzon musaman na Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Mali ya je birnin Kidal domin ganewa idanunsa halin da yankin ke ciki.
Rahotanni dake fitowa daga birnin Bamako sun habarta cewa a jiya Lahadi Manzon musaman na Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Mali Muhamad Saleh Anadi Uf ya kai ziyara birnin Kidal domin nuna goyan bayansa ga Dakarun tsaro da Sulhu na MDD da kuma gudanar da bincike kan yanayin da Al'umma ke ciki a yankin.
Kafin tashinsa daga birnin Bamako, mista Anadi Uf ya ziyarci Sojojin Majalisar Dinkin Duniya da suka jikkata kuma suke jiya a Asibitin birnin Bamako.
A ranar Assabar da ta gabata, kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci Gwamnatin Mali da ta gudanar da binciken gaggauwa kan kisan da aka yiwa Dakarun sulhu na Majalisar guda 6 da Asalinsu 'yan kasar Guine ne a arewacin kasar.
a cikin bayanin da suka fitar, manbobin kwamitin sun bukaci Gwamnatin Mali da ta gaggauta gudanar da bincike tare kuma da zagulo wadanda suka kai hari da kuma yi musu hukumci kamar yadda doka ta tanada.
A ranar Juma'ar da ta gabata ce, kungiyar Ansarudin suka kai hari kan sansanin Dakarun sulhu na MDD a yankin Kidal dake Arewacin kasar, harin da ya yi sanadiyar mutuwar Sojoji 6 tare kuma da jikkatar wasu kimanin 30 na daban.