Gwamnatin Aljeriya Ta Bada Sanarwan Korar Dukkan Yan Daesh Daga Kasar
Sojojin Aljeriya sun kawo karshen samuwar yan ta'adda ta Daesh a kasar
Gwamnatin kasar Aljeriya ta bada sanarwan cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar korar dukkan yan kungiyar Daesh daga kasar. Tashar television ta Almayadeen ta ce wata majiya wacce ba ta son a bayyana sunanta, ta bayyana mata cewa jami'an tsaron kasar Aljeriya sun yiwa mayakan kungiuyar Daesh dirar mikiya ta kuma hanata tabbatar da samuwarta a kasar. Majiyar ta kara da cewa kungiyar ta rasa dukkan cibiyoyin da ta kafa a sassa daban daban na kasar.
Majiyar har'ila yau ta kara da cewa tun bayan kisan wani dan yawon shakatawa a kasar a shekara ta 2014 ne gwamnatin kasar ta Aljeriya take bin wadanda suka aikata kisan suna kuma samun nasara ganin bayansu. Kuma har yanzun, inji majiyar wannan aikin yana ci gaba.
Daga kashe majiyar ta kara da cewa sojojin kasar na kasa tare da tallafi daga mayakan sama suna ci gaba da nema duk inda yayan wannan kungiyar suka boye don ganin bayansu.