Kame Masu Kwadaitar Da Matasa Domin Shiga Kungiyoyin 'Yan Ta'adda A Tunusiya
Jul 08, 2016 08:39 UTC
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Tunusiya ta sanar da kame wasu mutane biyu da suke kwadaitar da matasa domin shiga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda musamman kungiyar ta'addanci ta Da'ish.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunusiya a jiya Alhamis ta fitar da sanarwar cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kame wasu mutane biyu da suka shahara a fagen kwadaitar da matasa domin shiga cikin kungiyar ta'addanci ta Da'ish a lardin Sidi Bouzid, kuma mutanen biyu 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish ce da ke mamaye da wasu yankunan kasar Libiya.
Tags