Mali : Sojojin Faransa Sun Sanya Matsin Lamba kan Mayakan Jihadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8014-mali_sojojin_faransa_sun_sanya_matsin_lamba_kan_mayakan_jihadi
Rundinar sojin Faransa ta ce ta sanya matsin lamba wa gungun mayakan jihadi a arewacin kasar Mali.
(last modified 2018-08-22T06:58:35+00:00 )
Jul 12, 2016 06:47 UTC
  • Mali : Sojojin Faransa Sun Sanya Matsin Lamba kan Mayakan Jihadi

Rundinar sojin Faransa ta ce ta sanya matsin lamba wa gungun mayakan jihadi a arewacin kasar Mali.

Wannan matakin dai a cewar rundinar nada nufin hana hadewar mayakan dama karya laggon su kamar yadda wata majiyar sojin ta sanar.

Hare haren da mayakan ke kaiwa kan tawagar wazarda zamen lafiya ta MDD a Mali wato MINUSMA dama sojojin kasar ta Mali sun kara matuka a watannin baya bayan nan a yankin Kidal dake arewa maso gabashin Kasar.

Minisma dai na zamen tawagar MDD dake kasancewa a cikin yanayi mafi hadari daga cikin takwarorinta 16 dake jibge inda ta rasa dakarunta 27 a cikin shekara guda, saboda rashin kayan aiki na kariya masu sulke da kuma bayanan siri.