Mali
Mali: Neman Kira Ga Jami'an Gwamnatin Gao Su yi Murabus.
Mazauna birnin Gao da ke arewacin kasar Mali sun bukaci jami'an da ke tafiyar da iko a yankin nasu da su yi murabus.
Mazauna garin sun gudanar da Zanga-zanga, inda su ka bukaci masu taifyar da sha'anin mulki da kuma tsaro a yankin da su sauka daga kan mukamansu.
Wannan kiran dai ya biyo bayan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa mutane 3 ne a yankin a ranar talatar da ta gabata.
Wani ma'aikacin gwamnatin yankin ta Gao mai suna Muhammadu Tambora, ya ce; tun ranar talata harkoki sun tsaya cak a yankin. An rufe kasuwanni, kuma Bankuna ma sun dakatar da ayyukansu.
Mutanen yankin na Gao dai suna nuna rashin amincewarsu ne da sabuwar gwamnatin rikon kwarya ta yankin.
A gobe juma'a ne kuma ake sa ran cewa sabuwar gwamnatin za ta fara aikin nata.