Afirka Ta Kudu : Gobara Ta Kashe Mutane 8 A Gidan Marayu
Jul 14, 2016 11:57 UTC
Rahotanni daga Afirka ta kudu na cewa mutane takwas suka mutu a wata gobara da tashi a wani gidan marayu a birnin Durban.
Shida daga cikin wadanda suka rasa rayukan su a gobarar a cikin daren jiya Laraba yara ne wanda karaminsu dan shekaru takwas ne.
Ko baya ga wadanda suka rasa rayukan su akwai wasu mutane 14 da suka ji rauni amma yanayin baya cikin damuwa kamar yadda kakakin ma'aikatar kwana kwana a yankin KwaZulu-Natal ya shaidawa masu aiko da rahotanni.
Har kayo yanzu dai ba'a bayana musabibin tashin gobara ba, aman tuni 'yan kwana kwana suka shawo kan ta.
Ko a watan fabrairu 2010 an fuskanci wata gobara a wani gidan marayu yankin wace tayi sanadin mutuwar yara 13.
Tags