Ta'addanci ya fi ritsawa da musulmi a Duniya
(last modified Sun, 17 Jul 2016 06:14:40 GMT )
Jul 17, 2016 06:14 UTC
  • Ta'addanci ya fi ritsawa da musulmi a Duniya

Shugaban Kasar Senegal ya ce mafi yawan mutanan da ta'adanci ya ritsa da su musulmi ne.

A yayin Hirar sa da tashar telbijin din kasar Faransa Fance 24 a wannan Assabar, Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya tabbatar da cewa mafi yawan mutanan da harin ta'addanci ya ritsa da su a Duniya, musulmi, idan kuma ana son yakar ta'addanci wajibi ne a samu hadin kai da kuma tuntubar juna tsakanin kasashen musulmai, matukar hakan bai samu ba, abin bakin ciki, za a ci gaba da fuskantar ta'addanci kamar yadda ya faru a lokacin bikin tunawa da ranar 'yanci a birnin Nice da ke a Kudancin Faransa.

A Cikin daren ranar Alhamis ne da misalin karfe 11 na dare, direban wannan babbar mota ya kutsa kai cikin dandazon daruruwan mutane da suka taru a wannan birni dan kallon wasan wuta da aka saba yi a irin wannan rana. Ya dai share kusan tsawon kilomita biyu yana tafiya da motar kan al'umma inda ya hallaka mutane sama da 80 tare kuma da jikkata wasu dariruwa, kafin daga bisani 'yan sanda su harbe shi.