Komawar Dubban 'Yan kasar Uganda mazauna Sudan Ta Kudu gida
Komawar Dubban 'Yan kasar Uganda mazauna Sudan Ta Kudu gida.
Dubban 'yan asalin kasar Uganda sun koma gida daga kasar Sudan ta Kudu.
Cibiyar Watsa labaru ta "Africa Times' ta ambaci cewa; Ayarin motocin da ke dauke da 'yan kasar ta Uganda su 1000 da sojoji su ke yi wa rakiya, sun fice daga birnin Juba, inda su ka ratsa ta garin Nimule da ke kudancin Sudan, sannan suka ketara iyaka zuwa kasarsu.
Ministan harkokin wajen kasar Uganda, Henry Okello ya ce; sojojin kasar ne su ke da alhakin fito da 'yan Uganda fiye da 4000 mazauna kasar Sudan ta kudu da maida su gida.
Bugu da kari, ministan harkokin wajen na Uganda ya ce; Sojojin kasar tasa sun kuma taimakawa 'yan kasashen Jamus da China wajen fito da su daga cikin kasar Sudan ta kudu.
Uganda ta aike da sojoji a 2013 zuwa kasar Sudan ta Kudu, domin bada kariya ga shugaban kasar Silva Kiir, sai dai ta janye su a karshen 2015.
Fadan da ya barke makwanni biyu da su ka gabata a tsakanin sojoji magoya bayan shugaban kasa da kuma mataimakinsa ya ci rayukan fiye da mutane 300.