Masu da'awar Jihadi sun kwace wani sansanin Soja a kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8359-masu_da'awar_jihadi_sun_kwace_wani_sansanin_soja_a_kasar_mali
Wasu da ake zargi masu jihadi cikin motoci da babura sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke tsakiyar Mali wato a garin Nampala, inda suka karbe iko da yankin
(last modified 2018-08-22T06:58:37+00:00 )
Jul 19, 2016 11:53 UTC
  • Masu da'awar Jihadi sun kwace wani sansanin Soja a kasar Mali

Wasu da ake zargi masu jihadi cikin motoci da babura sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke tsakiyar Mali wato a garin Nampala, inda suka karbe iko da yankin

Wasu da ake zargi masu jihadi, sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke tsakiyar kasar Mali a birnin Nampala. A cewar magajin wani gari da ke kusa da yankin ya ce "Mayakan sun zo da manyan motoci hudu wasu kuma a kan babura, amma dakarun gwamnatin na sake jan damara a birnin Diabaly dan kwace iko da sansanin."

Kimanin sojoji 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikata a harin. A shekara ta 2013, kasar Faransa ta jibge dakarunta a kasar Mali da nufin fatattakan mayakan da ke yunkurin mamaye arewacin Mali.

A ranaikun 14 zuwa 17  kungiyoyin 'yan Tawayen Arewacin Mali sun gudanar da taro a Birnin Yamai na Jumhoriyar Nijer bisa Jagorancin Firaministan Kasar Briji Rafini, a karshen Taron sun fitar da sanarwar Bai daya, inda suka dauki kudirin karfafa matakan tsaron gagguwa da nufin kare arewacin kasar musaman garin Kildal dake fama da hare hare a baya bayan nan.