An Dawo Da Dokar Ta Baci A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8443-an_dawo_da_dokar_ta_baci_a_mali
Hukumomi a kasar Mali sun dawo da dakor ta bacin data kawo karshe a makon jiya, biyo bayan harin da aka kai a wani barikin sojin Nampala da ke tsakiyar kasar inda dakarun sojan kasar 17 suka rasa rayukansu.
(last modified 2018-08-22T11:28:38+00:00 )
Jul 21, 2016 09:29 UTC
  • An Dawo Da Dokar Ta Baci A Mali

Hukumomi a kasar Mali sun dawo da dakor ta bacin data kawo karshe a makon jiya, biyo bayan harin da aka kai a wani barikin sojin Nampala da ke tsakiyar kasar inda dakarun sojan kasar 17 suka rasa rayukansu.

Shugaba Ibrahim Boubakar Keita na Mali

Haka zalika hukumomin kasar sun ayyana zamen makoki na tsawan kwanaki uku daga wannan Alhamis. 

Mutanen dauke da makamai sun kai harin ne a ranar Talata data gabata a barikin sojin na Nampala inda dakarun sojan kasar 17 suka rasa rayukansu a yayinda wasu sama da 30 suka jikkata.

Dakarun sojin kasar Mali a fagen daga

Har kawo yanzu dai ba'a da tabas kan ko suwa keda alhakin kai harin, kasancewar kungiyoyi biyu ne suka sanar da daukan alhakin kai harin.

Da farko dai wata kungiyar dake faffatukar tabbatar da 'yancin Fulani tare da adalci (ANSIPRJ) da aka kafa a watan Yunin da ya gabata bayan wani hari da aka kai wa fulanin ta daukai nauyin kai harin.

Sai kuma daga bisani kungiyar Macina ta Ansar din ita ma ta sanar da daukan alhakin kai harin.