Rikici mai tsakani a arewacin Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8482-rikici_mai_tsakani_a_arewacin_mali
A Yayin da ake cikin yanayi na dokar ta bace a kasar Mali, wani rikici ya sake barkewa tsakanin 'yan tawayen abzunawa dake goyon bayan Gwamnati da masu adawa da ita a garin Kidal dake arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 22, 2016 03:38 UTC
  • Rikici mai tsakani a arewacin Mali

A Yayin da ake cikin yanayi na dokar ta bace a kasar Mali, wani rikici ya sake barkewa tsakanin 'yan tawayen abzunawa dake goyon bayan Gwamnati da masu adawa da ita a garin Kidal dake arewacin kasar.

Tashar Telbijin France 24 ta habarta cewa kwanaki biyu bayan harin da wasu da ake kyautata zaton masu da'awar Jihadi ne suka kai a sansanin Sojin Nampala dake tsakiyar Mali,wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar Sojoji 17, Shugaban kasar Ibrahim Boubakar Kieta ya kai ziyara wannan sansani domin yiwa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta'aziya, a yayin wannan ziyara wani rikici mai tsanani ya barke tsakanin 'yan tawayen abzunawa masu goyon bayan Gwamnati da masu adawa da ita a garin kidal na arewacin kasar,

Karar bindiga ya tilastawa Al'ummar yankin zama a gidajensu. bayan harin na sansanin sojin garin Nampala, Gwamnatin kasar ta shelanta zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar gaba daya.

Wannan rikici na zuwa ne a yayin da kasar ke cikin yanayi na dokar ta bace na kwanaki 10.