An Kashe Mutane Biyu Akan Iyakokin Aljeriya Da Tunisiya
Sojojin Tunisiya Sun Sanar da kashe 'yan bindiga biyu akan iyakokin kasar da Aljeriya
Kamfanin Dillancin Labarun Reuters daga kasar Tunisiya ya ambato cewa; A wani taho mu gama da sojojin kasar su ka yi da 'yan bindiga a yankunan "Jabal' da "Burbah" da "Junduwiyyah' sun kashe 'yan bindiga biyu, yayin da soja guda kuma ya jikkata.
Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa; Ana ci gaba da musayar wuta a tsakanin sojojin kasar ta Tunisiya da kuma 'yan bindiga a tuddan "Junduwiyyah' da ke kan iyaka da kasar ta Aljeriya.
Tun a cikin shekarar 2015 ne dai da 'yan ta'adda su ka kai mummunan hari akan masu yawon bude ido na waje da kuma dakarun tsaron fadar shugaban kasa, sojojin kasar ta Tunisiya su ka shiga halin ko ta kwana.