Musulmin Kasar Uganda Sun Bukaci Kafa Musu Ma'aikata Ta Musamman
(last modified Fri, 29 Jul 2016 11:19:27 GMT )
Jul 29, 2016 11:19 UTC
  • Musulmin Kasar Uganda Sun Bukaci Kafa Musu Ma'aikata Ta Musamman

Shugabannin Musulmin Kasar Uganda, Sun Bukaci Gwamnatin Kasar da ta Kafa Musu Ma'aikata ta musuamman

Kamfanin Dillancin Labarun "Ikna" ya ambato Majid Bagalalyvv, wanda shi ne shugaban kwamitin Zakka na kasar Uganda, yana fada a jiya alhamis cewa; "Shugabannin musulmin Uganda sun bukaci shugaban kasar Yoweri Museveni da ya kafa wata ma'aikata ta musamman wacce za ta rika kula da al'amurran musulmi.

Majid Bagalalyvv ya ci gaba da cewa; Shugabannin musulmi a birnin Kamfala ne su ka gabatar da shawarar ta kafa ma'aikata ta musamman wacce za ta kula da ayyukansu, sai dai har yanzu ba su sami jawabi ba.

Shugaban kwamitin Zakkar ya kuma  yi suka akan karancin musulmin da ake da su a cikin ayyukan gwamnati.

Shi ma shugaban musulmin birnin Kamfala Idris Lvsvaby ta ce; Da akwai musulmi da adadinsu ya kai miliyan 10 a cikin kasar ta Uganda, saboda haka suna da bukatuwa da ma'aikata ta musamman da za ta rika kula da lamurarransu.