MDD Ta Bukaci Karin Hadin Kai Don Fada Da Kungiyar Boko Haram
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatocin kasashen duniya da su kara ba da hadin kai wajen fada da kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram da ta addabi wasu kasashen Yammacin Afirka.
Mataimakin babban sakataren MDD kan harkokin siyasa Jeffrey Fieltman ne yayi wannan kiran a wani zama da kwamitin tsaron MDD ya gudanar inda ya ce ko shakka babu dakarun hadin gwiwa na kasashen yankin da suka hada da Nijeriya, Chadi, Kamaru, Nijar da kuma Benin sun sami nasarar fatattakan 'yan Boko Haram din daga yankuna masu yawan gaske, to sai dai kasashen suna bukatar karin taimako da goyon bayan kasashen duniya wajen fada da kungiyar ta Boko Haram.
Mataimakin babban sakataren MDD ya kara da cewa akwai bukatar kasashen duniya su kara kaimi wajen taimakawa wadannan kasashen a fadar da suke yi da annobar kungiyar ta Boko Haram.
A kwanakin baya ma dai mataimakin babban sakataren MDD kan harkokin ba da agaji Stephen O'bryan ya bukaci kasashen duniya da su kai daukin gaggawa ga yankunan da rikicin Boko Haram din ya daidaita musamman a Nigeria saboda matsalar yiyuwar bullar yunwa a yankunan.
Dakarun Nijeriya din dai sun sami nasarar karya lagon 'yan Boko Haram din a yankunan jihohin Arewa maso gabashin kasar inda 'yan Boko Haram din suka fi baje kolinsu, to sai dai har ya zuwa yanzu akwai sauran gyauronsu.