Majalisar Dokokin Tunusiya Ta Kada Kuri'ar Rashin Amincewa Da Majalisar Ministocin Kasar
A zaman da Majalisar Dokokin Tunusiya ta gudanar a jiya Asabar ta kada kuri'ar rashin amincewa da Majalisar ministocin kasar karkashin jagorancin fira minista Habib Essid lamarin da ya kawo karshen gwamnatinsa.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa rahoton cewa: A zaman da 'yan Majalisun Dokokin Tunusiya suka gudanar a yammacin jiya Asabar da nufin kada kuri'arsu kan matsayin Majalisar ministocin kasar, 'yan majalisu 118 sun kada kuri'ar rashin amincewa da ci gaba da kasancewar majalisar karkashin jagorancin fira minista Habib Essid. yayin 'yan majalisu uku kacal suka kada kuri'ar amincewa da ita, wasu 27 na daban kuma suka ki bayyana matsayinsu..
A jawabin da ya gabatar a gaban Majalisar Dokokin Tunusiya a bayan kin amincewa da Majalisar ministocinsa: Fira minista Habib Essad ya yi furuci da cewa tuni da ma yana da masaniyar 'yan Majalisun zasu rusa Majalisar Ministocin kasar.
Rushewar Majalisar Ministocin Tunusiya karkashin fira minista Habib Essid ta zo ne bayan jagorancin shekara daya da rabi sakamakon matsalolin tattalin arziki da na tsaro da kasar ke ci gaba da fuskanta. Sannan a gobe Litinin ne ake sa ran fara gudanar da muhawarar zaben sabon fira minista da zai jagoranci gwamnatin kasar ta Tunusiya.