Senegal : Macky Sall Ya Janye Bukatarsa Ta Rage Wa'adin Mulkinsa
-
Macky Sall shugaban kasar Senegal
Hakan dai ya biyo bayan da kotun kolin kasar tayi watsi da bukatar rage mulkin nasa daga shekara 7 zuwa 5.
Shugaban Macky Sall na Senegal ya sanar da janye bukatarsa ta rage wa'adin mulkin sa daga shekara bakwai zuwa shekara biyar.
Hakan dai ya biyo bayan da kotun kolin kasar tayi watsi da bukatar rage mulkin nasa da shekara biyu.
A wani jawabinsa ga al'ummar kasar da yammacin jiyya Talata Mr Sall, ya ce zai ci gaba da aikin sa har zuwa karshen wannan wa'adin sa dake karewa a shekarar 2019, aman ya ce zai sa a gudanar da zaben jin ra'ayoyin jama'a a ranar 30 ga watan Maris mai zuwa.
Batun rage wa'adin mulki shugaban kasa a Senegal, na daga cikin al'kawulan da shugaba Maky Sall ya dauka a lokacin yakin neman zabensa.