Mali : An Tsawaita Dokar Ta Baci Da Watanni Takwas
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8959-mali_an_tsawaita_dokar_ta_baci_da_watanni_takwas
Majalisar dokoki a Mali ta amunce da tsawaita dokar ta baki da watannin takwas a wannan kasa dake fama da tashe tashen hankula masu nasaba da na kungiyoyin jihadi da na gungun masu dauke da makamai.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jul 31, 2016 11:43 UTC
  •  Mali : An Tsawaita Dokar Ta Baci Da Watanni Takwas

Majalisar dokoki a Mali ta amunce da tsawaita dokar ta baki da watannin takwas a wannan kasa dake fama da tashe tashen hankula masu nasaba da na kungiyoyin jihadi da na gungun masu dauke da makamai.

An dai jima ana tsawaita dokar ta baci a wannan kasa ta mali tun dai bayan harin da wasu mayakn jihadi suka kai kai a otel Radisson Blu dake Bamako a ranar 20 ga watan Nuwamba bara, inda mutane akallah 20 suka mutu.

Dokar ta baki da aka kafa a bayan bayan nan wace ke kawo karshe a yau lahadi ita ce ta kwanaki goma bayan harin da wasu masu daukeda nakamai suka kai a barikin soji na Nampala, inda sojojin kasar 17 suka rasa rayukan su.

Tsawaita dokar ta baci a cewar hukumomin kasar zai taimakawa sojojin kasar kwarai da gaske wajen tafiyar da aikin su ba dare ba rana a fadin kasar.

Tsawaita wannan dokar ta baci ta zo ne a daidai lokacin da sabon rikici ya kunno kai tsakanin 'yan tawaye dake fada da juna a yankin Kidal dake arewacin kasar.