Zuma Ya Bukaci Fitowar Al'ummar Afirka Ta Kudu A Zabukan Kananan Hukumomin
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i8977-zuma_ya_bukaci_fitowar_al'ummar_afirka_ta_kudu_a_zabukan_kananan_hukumomin
Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya bukaci al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu a zabukan kanan hukumomin da za a gudanar a kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:41+00:00 )
Aug 01, 2016 05:54 UTC
  • Zuma Ya Bukaci Fitowar Al'ummar Afirka Ta Kudu A Zabukan Kananan Hukumomin

Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya bukaci al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu a zabukan kanan hukumomin da za a gudanar a kasar.

Shugaba Zuma ya yi wannan kira ne a gaban taron jam'iyyar ANC mai mulki a kasar, inda ya yi ishara da cewa, bisa la'akari da gwagwarmayar da al'ummar kasar suka yi domin samun 'yancin kai da fita daga kangin mulkin bauta da wariyar launin fata, ya zama wajibi su kare wannan gwagwarmaya ta hanyar tabbatar da dimukradiyarsu.

Wannan kira na Jacob Zuma dai ya zo ne a daidai lokacin da wasu daga cikin 'yan siyasar kasar daga jam'iyyar ANC mai mulki suke fuskantar tuhumce-tuhumce kan batutuwa da suka danganci cin hanci da rashawa, wanda hakan ka iya rage tasirin nasarorin da ake ganin 'yan talarar jam'iyyar za su samu a zabuka masu zuwa.

Jam'iyyar Democratic Union ita ce jam'iyyar adawa mafi girma a kasar Afirka ta kudu, kuma a wanann karon tana hankoron ganin ta samu gagarumin rinjaye a yankin Kapetown.