Sojojin Nijeriya Sun Dakile Wani Shirin Kai Harin Kungiyar Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9037-sojojin_nijeriya_sun_dakile_wani_shirin_kai_harin_kungiyar_boko_haram
Sojojin Nijeriya da dakarun sa kai na JTF sun sami nasarar dakile wani shirin da kungiyar Boko Haram ta yi na kai wani mummunan hari a wajen birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda suka hallaka 'yan kungiyar ta'addancin su biyar.
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Aug 02, 2016 06:50 UTC
  • Sojojin Nijeriya Sun Dakile Wani Shirin Kai Harin Kungiyar Boko Haram

Sojojin Nijeriya da dakarun sa kai na JTF sun sami nasarar dakile wani shirin da kungiyar Boko Haram ta yi na kai wani mummunan hari a wajen birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda suka hallaka 'yan kungiyar ta'addancin su biyar.

Kakakin rundunar sojin ta Nijeriya Kanar Sani Usman Kukasheka ne ya sanar da hakan inda ya ce dakarun wadanda suka cikin shirin nan na Operation Lafiya Dole sun sami nasarar tarwatsa bakar aniyar ta kungiyar Boko Haram a yankin Yauri da ke wajen birnin Maidugurin, inda baya ga wadanda aka kashe din har ila yau sojojin sun sami nasarar kwace wani adadi mai yawa na makamai.

Tun bayan kafa sabuwar gwamnati a Nijeriyan, dakarun sojin kasar sun sami nasarar karya lagon 'yan kungiyar ta Boko Haram wadanda suka kaddamar da hare-haren na su a jihar ta Borno a shekara ta 2009 wanda kuma ya zuwa yanzu hakan ya janyo hasarar rayukan dubun dubatan al'ummar kasar musamman na jihar Bornon da sauran jihohin da suke makwabtaka da ita a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Rikicin na Boko Haram dai yayi sanadiyyar tarwatsa miliyoyin al'ummomin yankin da kuma sanya su cikin mawuyacin halin da ya sanya a kwanakin baya MDD ta bukaci kasashen duniya da su shigo cikin lamarin don hana fadawar mutanen yankin cikin tsaka mai wuya na yunwa.