Jam'iyyar ANC Mai Mulki Na Kan Gaba A Zaben Afirka Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9148-jam'iyyar_anc_mai_mulki_na_kan_gaba_a_zaben_afirka_ta_kudu
Rahotanni daga kasar Afirka ta kudu suna nuni da cewa jam'iyyar ANC mai mulki a kasar ita ce take kan gaba a zaben kananan hukumomin da ake gudanarwa a kasar duk kuwa da cewa akwai yiyuwar ta rasa wasu garuruwan a karon farko tun bayan da ta dare karagar mulki.
(last modified 2018-08-22T11:28:42+00:00 )
Aug 04, 2016 11:07 UTC
  • Jam'iyyar ANC Mai Mulki Na Kan Gaba A Zaben Afirka Ta Kudu

Rahotanni daga kasar Afirka ta kudu suna nuni da cewa jam'iyyar ANC mai mulki a kasar ita ce take kan gaba a zaben kananan hukumomin da ake gudanarwa a kasar duk kuwa da cewa akwai yiyuwar ta rasa wasu garuruwan a karon farko tun bayan da ta dare karagar mulki.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce ya zuwa yanzu an kidaya kashi daya cikin uku na kuri'un da aka kada din inda jam'iyyar ta ANC take kan gaba da kashi 50 cikin dari, sannan jam'iyyar Democratic Alliance (DA) take biye mata da kashi 34 cikin dari sai kuma jam'iyyar Economic Freedom Fighters da take da kashi 6 cikin dari.

A gobe Juma'a ce dai ake sa ran za a fadi sakamakon zaben gaba daya, inda da kididdigar da aka gudanar tana nuni da cewa jam'iyyar ANC din za ta samu rinjaye a zaben sai dai watakila ba zai kai kamar na zaben karshe da aka gudanar a shekara ta 2011 ba inda ta samu kashi 62 cikin dari ba.

Tun dai bayan da aka kawar da mulkin wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudun da kuma gudanar da zaben farko na demokradiyya a kasar a shekara ta 1994, jam'iyyar ANC din take mulki a kasar.