Gwamnatin Kasar Chadi Ta Hana Taron Zanga Zangar Yan Adawa
Gwamnatin Chadi ta haramtan zanga zangar jam'iyyun adawan kasar
Ma'aikatar cikin gida na kasar Chadi ta bada sanarwan haramta duk wani taro na yan adawa a duk fadin kasar. Kamganin dillancin labaran AFP ma kasar Faransa ya ce ma'aikatan ta bayyana wannan sanarwan ne a jiya Alhamis ta kuma kara da cewa zanga zangar da jam'iyyun adawa suka shirya gudanarwa a ranakun Asabar 6 ga watan Augusta da kuma Lahadi 7 ga watan an haramtasu a duk fadin kasar.
A ranar Litinin mai zuwa ne aka shirya gudanar bikin rantsar da shugaban Idris Debi a matsayin shugaban kasar karo na biyar a birnin Njamaina babban birnin kasar. Ana saran manya manyan baki daga kasashen waje da kuma daga cikin gida ne zasu halarci taron.
Jam'iyyun adawar kasar dai suna ganin shugaba Debi yayi magudi ne a zaben watan Afrilun da ya gabata kuma da sakamakon wancan zaben bai cancanci zama shugaban kasa ba. Har'ila yau sun bukaci a gudanar da sabon zabe.
Shugaban Idris Debi dai dan shekara 64 a duniya ya hau kan kujerar shugabancin kasar Chadi ne tun shekara 1990M.