Kashe Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya A Kasar Mali
Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Kashe Tare Da Jikkata Dakarun Sulhu Biyar A Mali.
Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato majiyar majalisar dinkin duniyar na cewa motar da take dauke da dakarun tabbatar da zaman lafiyar ta ci karo da nakiya a arewacin Mali, da hakan ya yi sanadin mutuwar daya daga cikinsu da kuma jikkatar wasu hudu.
Rudnunar tabbatar da zaman lafiyar ta majalisar dinkin duniyar da ake yi wa lakabi da "MINUSMA" ta fitar da bayanin da ke nuni da cewa an kai musu hari ne a lokacin da su ke yi wa wasu muhimman kayan aiki rakiya zuwa garin Agilhuk da ke gundumar Kidal.
Har ila yau, sanarwar ta kara da cewa bayan gushewar sa'oi biyu, wata nakiyar ta sake tashi sai dai ba ta haddasa asarar rayuka ba.
A ranar juma'ar da ta gabata ma dai kungiyar Ansaruddin ta dauki alhakin kai wani hari a kusa da garin Kidal akan sojojin kasar Chadi.