Akalla Sojojin Kasar Mali 5 Ne Suka Rasa Rayukansu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9379-akalla_sojojin_kasar_mali_5_ne_suka_rasa_rayukansu
A ci gaba da kaddamar da hare-hare da masu da'awar jihadi da ke da alka ada kungiyar Alkaida suke yi a Mali, wasu jami'an sojin kasar sun rasa rayukansu a wani hari da 'yan bindigar suka kai kansu.
(last modified 2018-08-22T06:58:44+00:00 )
Aug 09, 2016 17:07 UTC
  • Akalla Sojojin Kasar Mali 5 Ne Suka Rasa Rayukansu

A ci gaba da kaddamar da hare-hare da masu da'awar jihadi da ke da alka ada kungiyar Alkaida suke yi a Mali, wasu jami'an sojin kasar sun rasa rayukansu a wani hari da 'yan bindigar suka kai kansu.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga wani babban jami'in sojin kasar da ya  nemi a sakaya sunansa daga birnin Bamako a yau cewa, a daren jiya wasu 'yan ta'adda na kungiyar Ansaruddin mai alaka da alkaida, sun kaddamar da wani hari kan wani sansanonin sojin kasar a yankin Mopti, inda suka kashe 5 daga cikin sojojin.

Haere-haren 'yan bindigar na kara tsananta nea  kasar mali, a daidai lokacin da shugaban kasar ya kara tsawaita dokar ta faci a kasar har na tsawon watanni uku a nan gaba.

A makon da ya gabata ma wasu masu dauke da makamai sun kashe wani babban jami'in 'yan sandan kasar a yankin arewa maso yammacin kasar.