Ana Jiran Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Da 'Yan Majalisa A Kasar Zambiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9496-ana_jiran_sakamakon_zaben_shugaban_kasa_da_'yan_majalisa_a_kasar_zambiya
Al'ummar kasar Zambiya na ci gaba da jiran dakon sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar kasar da aka gudanar a jiya Alhamis a zaben da ake kankankan tsakanin shugaban kasar Edgar Lungu da abokin hamaiya Hakainde Hichilema da ke zargin shugaban da lalata tattalin arzikin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:45+00:00 )
Aug 12, 2016 00:30 UTC
  • Ana Jiran Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Da 'Yan Majalisa A Kasar Zambiya

Al'ummar kasar Zambiya na ci gaba da jiran dakon sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar kasar da aka gudanar a jiya Alhamis a zaben da ake kankankan tsakanin shugaban kasar Edgar Lungu da abokin hamaiya Hakainde Hichilema da ke zargin shugaban da lalata tattalin arzikin kasar.

Rahotanni daga kasar Zambiyan sun ce  tun a jiya alhamis din ne dai aka rufe rumfunan zabe bayan da 'yan kasar suka kada kuri'unsu a dogayen layuka a rumfunan kada kuri'un da aka tanadar a duk fadin kasar ba tare da tashin hankali ba.

Duk da cewa ba a sanar da adadin mutanen da suka fito kada kuri'un na su ba, to sai dai rahotanni sun ce al'umma sun fito sosai a yayin zaben, da cibiyoyin kasa da kasa suka sanya ido kansa ciki kuwa har da kungiyar Tarayyar Afirka wacce ta tura tawaga karkashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, wanda  ya bayyana jin dadinsa da yadda zaben ya gudana.

A zaben da aka gudanar a  kasar watanni 20 da suka gabata don cike gibin shugaban kasar bayan mutuwar tsohon shugaban kasar Michael Sata, shugaba mai ci yanzu Edgar Lungu ya kada abokin hamayyar nasa  Hakainde Hichilema.

Hukumar zaben kasar dai ta ce tana sa ran a gobe Asabar ko kuma da duku-dukun jibi Lahadi ne za a sanar da sakamakon zaben na karshe.