Mutanen Uganda Sun Fara Kada Kuri'a A Zaben Shugaban Kasa A Kasar
Rahotanni daga kasar Uganda sun bayyana cewar al'ummar kasar sun fara kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da ake gudanarwa a yau din nan Alhamis, da ake ganin shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni ne zai lashe zaben.
Rahotannin sun ce an samu jinkiri wajen fara kada kuri'un da awanni biyar a wasu rumfunan zaben a birnin Kampala babban birnin kasar a yayin da jama’a suke ci gaba da jira a rumfunan zaben.
‘Yan takara bakwai ne dai ke kalubalantar shugaba Museveni duk da cewa babban kalubalen da yake fuskanta daga wajen madugun 'yan adawan kasar ne Kizza Besigye wanda tun da fari ma ya sanya shakkun kan yiyuwar za a gudanar da ingantaccen zabe a kasar.
Shugaba Yoweri Museveni dan shekaru 71 ya shafe kimanin shekaru 30 akan karagar mulkin kasar.