Rikici ya barke tsakanin Matasa da 'yan sanda a Kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i9775-rikici_ya_barke_tsakanin_matasa_da_'yan_sanda_a_kasar_mali
Wani sabon rikici ya barke tsakanin Matasa masu adawa da kamun wani Jaridar wata Radio mai suna muhamad Yusuf a Bamako babban birnin kasar Mali
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 17, 2016 13:28 UTC
  • Rikici ya barke tsakanin Matasa da 'yan sanda a Kasar Mali

Wani sabon rikici ya barke tsakanin Matasa masu adawa da kamun wani Jaridar wata Radio mai suna muhamad Yusuf a Bamako babban birnin kasar Mali

kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto majiyoyin watsa labaran kasar Mali na cewa a wannan Laraba rikici ya barke a gaban kotun dake kokarin hukunta wani Jaridar  Radio mai suna muhamad Yusuf a Bamako babban birnin kasar , lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu da dama na daban.

Gwamnati ta kame Muhamad Yusuf ne bisa zarkin sa da laifin cin mutunci ga shugaban kasa gami da jami'an tsaron kasar, inda a wani shiri da ya gabatar a Radio, ya soki lamirin Shugaban kasar Ibrahim Boubakar Kieta sannan kuma ya bayyana irin kashin da Dakarun tsaron kasar suka sha a hanun  masu tayar da kayar baya.

A shafin sa na yanar gizo, Muhamad Yusuf ya bukaci Al'ummar kasar da su gudanar da zanga-zangar goyon bayansa yau Laraba, a yayin da zai  gurfanar a gaban kuliya.