Chadi : 'Yan Adawa Na Bukatar Tattauna Da Masu Mulki
(last modified Sat, 20 Aug 2016 10:58:32 GMT )
Aug 20, 2016 10:58 UTC
  • Chadi : 'Yan Adawa Na Bukatar Tattauna Da Masu Mulki

'Yan adawa a Chadi sun bukaci tattaunawa ta keke da keke da masu mulkin kasar, kwanaki goma bayan rantsar da Idriss deby Itmo a wa'adi mulki na biyar a shugabancin kasar.

Da yake karin haske dangane da hakan, jagoran 'yan adawa na kasar Saleh Kebzabo, ya ce a shirye suke domin tattaunawa da duk bangarorin siyasa na kasar, don samun mafita a rikicin siyasa kasar.

Saidai ya ce suna bukatar hakan tare da halatar abokan hulda na kasar wadanda suka saba damawa dasu a cikin irin wannan yanayi.

A yayin jawabin rantsar dashi ne Idris Deby ya yi kira ga 'yan adawan akan hada karfi don ciyarda kasar a gaba.

Rikicin siyasa ya yi kamari a wannan kasar ta Chadi tun dai bayan da Shugaba Idriss Deby ya sake lashe zaben kasar na watan Afrilu da kashi 59%, zaben da 'yan adawa suka ce yana cikeda magudi.