-
An Gudanar Da Taro Kan Matsalar Karamcin Abinci A Afirka
Sep 07, 2018 07:41A cikin wannan mako ne kwararru a fannin harkokin noma na Afirka suka gudanar da taro a birnin Kigali , inda suka yi gargadin cewa matsalar sauyin yanayi da kuma yaduwar tsutsotsi na barazanar haddasa matsalar karancin abinci a Nahiyar Afirka.
-
Libya: Jami'an Diplomasiyyar Kasashe Da Dama Sun Fice Daga Tripoli
Sep 07, 2018 01:09Kafafen watsa labaran kasar Libya sun ce ficewar jami'an diplomasiyyar ya biyo bayan fadan da aka dauki mako guda ana yi a tsakanin bangarorin da suke dauke da makamai
-
Sojojin Nijeriya Sun Ce Sun Hallaka 'Yan Boko Haram Da Dama
Sep 06, 2018 12:12Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa dakarunta sun sami nasarar hallaka wani adadi mai yawa na 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
-
An Daure Wasu Sojojin Sudan Ta Kudu Saboda Samunsu Da Laifin Fyade Da Kisan Gilla
Sep 06, 2018 12:11Wata kotun soji a kasar Sudan ta Kudu ta yanke wa wasu sojoji guda 10 hukuncin dauri a gidan maza saboda samunsu da laifin yin fyade wa wasu mata masu ba da agaji bugu da kari kan kashe wani dan jarida a wani hari da suka kai wani hotel a birnin Juba, babban birnin kasar a shekara ta 2016.
-
Mahukunta A Kenya Sun Kori Wani Dan Kasar China Da Ya Kira Mutanen Kasar Da 'Birrai'
Sep 06, 2018 12:11Mahukunta a kasar Kenya sun kori wani dan kasar China mai suna Liu Jiaqi daga kasar bayan wani faifan bidiyo da yayi kuma ya watsa yana bayyana al'ummar kasar ciki kuwa har da shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin birrai.
-
Jami'an Tsaro A Najeriya Suna Zargin Akwai Wakilan Kunkiyar Daesh A Sansanon Yan Gudun Hijira A Kasar
Sep 06, 2018 07:21Rundunar yansanda a Najeriya ta bayyana cewa akwai wakilan yan kungiyar Daesh a sansanonin yan gudun hijira a yankin arewa maso gabacin kasar.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Yan Siyasa A Mauritaniya Su Warware Sabani Tsakaninsu Ta Hanyar Tattaunawa
Sep 06, 2018 07:17Babban sakataren MDD Antony Gutteres ya bukaci gwamnatin kasar Mauritania da jam'iyyun adawar kasar su warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa.
-
An Ceto Bakin Haure Sama Da 400 A Arewacin Kasar Nijer
Sep 06, 2018 03:52Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta ce cikin kwanaki biyu ta ceto bakin haure sama da 400 a cikin yankin Sahara na kasar Nijer dake kan iyaka da kasar Aljeriya
-
Cutar Ebola Na Ci Gaba Da Kisa A Kasar D/Congo
Sep 06, 2018 03:51Hukumomin jamhoriyar Congo sun sanar da mutuwar mutane da dama a lardin Butembo da ke yankin gabashin kasar sakamakon cutar Ebola.
-
Shugaban Kasar Mali Ya Jaddada Aniyarsa Ta Tabbatar Da Zaman Lafiya Da Sulhu A Kasar
Sep 05, 2018 14:38Shugaban kasar Mali ya jaddada aniyar sabuwar gwamnatinsa ta tabbatar da zaman lafiya da sulhu a yankin arewacin kasar da ke fama da tashe-tashen hankula.