-
A Yau Ne Aka Bude Gasar Kur'ani Ta Duniya A Kasar Masar
Mar 24, 2018 07:21An bude babbar gasar kur'ani ta duniya a kasar Masar tare da halartar daruruwan makaranta daga kasashen duniya 50.
-
Sabon Rikicin Ya sake Kunno Kai A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
Mar 24, 2018 07:21Rahotanni daga jahuriyar Afirka ta tsakiya sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon artabun da aka yi tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a yankunan arewa maso yammacin kasar.
-
Babbar Jam'iyyar Adawa A Sudan Ta Bukaci Murabus Din Shugaban Kasar
Mar 24, 2018 02:01Jam'iyyar Ummah da take matsayar babbar jam'iyyar adawa a Sudan ta bukaci shugaban kasar Umar Hasan Albashir kan ya dauki matakin yin murabus daga kan karagar shugabancin kasar.
-
Shugaban Kasar Masar Ya Dauki Alkawarin Kawo Karshen 'Yan Ta'adda A Yankin Sina
Mar 24, 2018 01:58Shugaban kasar Masar ya jaddada cewa cikin dan gajeren lokaci sojojin gwamnatin Masar zasu kawo karshen duk wata kungiyar ta'addanci a yankin Sina.
-
An Yi Taho Mu Gama Tsakanin 'Yan Sanda Da 'Yan Adawa A Guine Konakiry
Mar 23, 2018 13:15'Yan adawar kasar Guine konakiry sun yi taho mu gama da jami'an 'yan sanda yayin da suke gudanar da zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zabe.
-
Kamaru: An Kai Hari Kan Wata Ma'aikata A yankin Dake Amfani Da Turancin Ingilishi
Mar 23, 2018 13:12Majiyar tsaron kasar kamaru ta samar da kashe wani ma'aikacin gwamnati a yayin da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wata tawagar ma'aikata a yankin da ake amfani da turancin Ingilishi
-
Nijer:'Yan Boko Haran Sun Kashe Mutane 7 A Jahar Diffa
Mar 23, 2018 13:09Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton' yan Boko Haram ne sun kai wani hari a kauyen Tumur dake jihar Diffa a cikin daren jiya wayewar wannan safiyar Juma’a inda suka kashe mutum bakwai tare da jikattaa wasu da dama na daban.
-
Zimbabwe: An Yi Afuwa Ga Fursunoni Masu Yawa Da Ke Tsare A Gidajen Kaso
Mar 23, 2018 07:50Hukumomin da ke kula da lamurran gidajen kaso a kasar Zimbabwe sun sanar da cewa, gwamnatin kasar ta amince a yi wa fursunoni dubu uku afuwa.
-
Gabon : An Sake Hana Jagoran 'Yan Adawa Fita Kasar Waje
Mar 23, 2018 01:21Jami'an tsaro a Gabon sun sake hana jagoran 'yan adawa na kasar, Jean Ping, fita daga kasar, a daidai lokacin da yake shirin hawa jirgi don zuwa birnin Paris na kasar Faransa.
-
Somaliya : Bam Ya Kashe Mutum 14 A Mogadisho
Mar 22, 2018 23:37Hukumomi a Somaliya sun ce mutane a kalla 14 ne suka gamu da ajalinsu, kana wasu da dama suka raunana a wani harin bam da aka kai a gaban wani shahararren hotel a Mogadisho babban birnin kasar.