-
Ziyarar Aikin Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Rasha Ya Kai Zuwa Habasha
Mar 10, 2018 02:22Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya fara gudanar da ziyarar aiki a kasar Habasha, inda zai gana da mahukuntan kasar a kan batutuwa da dama musamman a fagen bunkasa harkar tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.
-
Goyon Bayan Da Mugabe Yake Nuna Wa 'Yan Adawa Ya Tada Kura A Zimbabwe
Mar 10, 2018 01:54Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun bayyana cewar goyon bayan da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe yake ba wa tsohon janar din sojin kasar da ke shirin kalubalantar jam'iyyar ZANU-PF mai mulki a zaben da za a yi nan gaba a kasar ya tayar da kura a kasar.
-
Sojojin Masar Sun Kashe 'Yan Ta'adda Sama Da 100 Tun Bayan Kaddamar Da Harin Sinai
Mar 10, 2018 01:54Kakakin rundunar sojin kasar Masar, Tamer El-Refaie, ya bayyana cewar rundunar sojin kasar ta sami gagarumar nasarar a watan farko na hare-haren da suka kaddamar da nufin tsarkake yankin Sinai na kasar daga 'yan ta'adda bayan da suka sami nasarar kashe sama da 'yan ta'adda 100 a yanki baya ga wadanda aka kama.
-
Gwamnatin Burkina Faso Ta Zargin Jami'an Tsohuwar Gwamnatin Kasar Da Ta'addanci
Mar 10, 2018 01:53Gwamnatin kasar Burkina Faso ta zargi wasu jami'an tsohuwar gwamnatin kasar ta tsohon shugaba Blaise Compaoré da hannu cikin hare-haren ta'addancin da kasar ta fuskanta.
-
An Cafke Jagororin 'Yan Adawa Biyu A Senegal
Mar 09, 2018 11:30'Yan sanda a birnin Dakar na Senegal na tsare da wasu jagororin 'yan adawa biyu, a yayin wata zanga-zanga da hukumomin kasar suka haramta.
-
Kenya : Uhuru Ya Gana Da Jagoran 'Yan Adawa
Mar 09, 2018 11:11Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya, ya gana da jagoran 'yan adawa na kasar Raila Odinga a karon farko tun bayan sake zabensa a matsayin shugaban kasar a watan Oktoba.
-
Harin Boko Haram Ya Lashe Rayukan Jami'an Tsaron Najeriya 10
Mar 09, 2018 08:16Shugaban 'Yan sandar jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin Najeriya ya sanar da mutuwar jami'an tsaron kasar 10 sanadiyar harin kungiyar boko haram.
-
Ziyarar Ministan Harakokin Rasha A Habasha
Mar 09, 2018 08:15Ministan harakokin wajen kasar Rasha ya kai ziyara zuwa kasar Ethiopia
-
Sojojin Libya Sun Baiwa 'Yan Ci Ranin Afrika Wa'adin Kwanaki 9 Da Su Bar Kasar
Mar 09, 2018 01:29Rundunar sojin kasar Libya ta bayar da wa'adin kwanaki 9 ga 'yan Afrika da suke cikin kasar ba bisa ka'ida ba, da su gaggauta barin kasar.
-
Kotun ICC Ta Yanke Hukunci A Kan Tsohon Madugun 'Yan Tawayen Congo
Mar 09, 2018 01:28Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta yanke hukunci a kan tsohon madugun 'yan tawayen Congo Germain Katanga, wanda aka same shi da hannu wajen cin zarafin jama'a da aikata laifukan yaki.