-
Djibouti : Jam'iyya mai Mulki Ta Yi Ikirarin Lashe Zaben 'Yan Majalisa
Feb 26, 2018 07:48Jam'iyya mai mulki ta (UMP) a Djibouti, ta yi ikirarin lashe zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka kada kuri'arsa a ranar Juma'a da ta gabata gagarimin rinjaye.
-
DRC : 'Yan Sanda Sun Musunta Amfani Da Harsashin Gaske Kan Masu Zanga-zanga
Feb 26, 2018 07:48'Yan sanda a Jamhuriya Demukuraddiyar Congo, sun musanta yin amfani harsashin bindiga na gaske kan 'yan katolika dake zanga-zanga.
-
Rundunar Sojin Saman Nijeriya Ta Sanar Da Tura Karin Jiragen Sama Don Neman 'Yan Matan Dapchi
Feb 26, 2018 02:16Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa ta kara tura jiragen sama da sauran na'urorin bincike zuwa yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriyan don ci gaba da neman 'yan matan makarantar mata ta Dapchi da suka bace bayan wani hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai makarantar a makon da ya wuce.
-
Kungiyar Tarayyar Turai Ta Yi Suka Kan Take Hakkin Bil-Adama A Kasar Tanzaniya
Feb 25, 2018 15:57Tawagar kungiyar tarayyar Turai da take ziyarar aiki a birnin Darus-Salam fadar mulkin kasar Tanzaniya ta yi kakkausar suka kan yadda take hakkokin bil-Adama yake kara yin kamari a kasar musamman a cikin 'yan watannin baya-bayan nan.
-
Ma'aikatar Ilimi A Aljeriya Ta Sanar Da Koran Dubban Malaman Makarantun Boko A Kasar
Feb 25, 2018 15:37Ma'aikatar ilimi da tarbiyya ta Aljeriya ta sanar da koran malaman makarantun boko kimanin dubu hudu daga aiki, bayan gudanar da yajin aiki ba a kan ka'ida ba.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Akwai Bakin Haure Fiye Da 700,000 A Kasar Libiya
Feb 25, 2018 15:25Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada labarin cewa: A halin yanzu haka akwai bakin haure da yawansu ya haura 700,000 da suka fito daga kasashe 40 na duniya a cikin kasar Libiya.
-
DRC : 'Yan Sanda Sun Yi Harbi Kan 'Yan Katolika Dake Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
Feb 25, 2018 07:22Rahotanni daga Jamhuriya Demukuraddiyar Congo na cewa mutane biyu suka raunana sakamakon harbi da bindiga da 'yan sanda suka yi kan 'yan Katolika dake zanga -zangar kin jinin gwamnati.
-
Somaliya : Yawan Mamata Bayan Harin Mogadishu, Ya Kai 32
Feb 25, 2018 07:21Hukumomin tsaron a Somaliya sun ce, yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin Mogadishu, babban birnin kasar ya karu zuwa 32.
-
Kura Ta Lafa A Birnin Bangui Na Afirka Ta Tsakiya Bayan Musayar Wuta Tsakanin 'Yan Bindiga
Feb 25, 2018 03:53Rahotanni daga birnin Bangui fadar mulkin jamhuriyar Afirka ta tsakiya na nuni da cewa kura ta lafa bayan musayar wutar da aka yi a ranar Juma'a da ta gabata a tsakanin wasu gungun 'yan bindiga da suke dauke da manyan makamai.
-
Bankin Raya Afirka Zai Bayar Bashin Dala Biliyan 2 Ga Morocco
Feb 25, 2018 03:48Bankin raya Afirka ya sanar da cewa zai bayar da bashin kudi har dalar Amurka biliyan biyu ga Morocco a cikin shekaru biyu, domin gudanar da wasu ayyuka na musamman a kasar.