-
Togo: 'Yan Adawa Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga
Dec 02, 2018 01:07Dubban 'yan adawa sun gudanar da zanga-zanga a ciki da wajen birnin Lome fadar mulkin kasar Togo, domin nuna rashin amincewa da gudanar da zaben 'yan majalisa.
-
Hukumar CAF Ta Kwace Damar Daukan Bakuncin Gasar Cin Kofin Afirka Daga Kasar Kamaru
Dec 01, 2018 01:54Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta sanar da kwace damar daukar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afirka (AFCON) na shekara ta 2019 da ta ba wa kasar Kamaru saboda alamu suna nuna cewa kasar ba ta shirya wa hakan ba.
-
Kungiyoyin EU Da ECOWAS Sun Bayyana Damuwarsu Kan Zafafa Hare-Haren Boko Haram
Dec 01, 2018 01:52Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS sun bayyana tsananin damuwarsu dangane da yadda kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram take kara zafafa hare-haren da take kai wa yankunan arewa maso gabashin Nijeriya.
-
MDD: An Barnata Kudin Hukumar 'Yan gudun Hijira A Uganda Da Sudan ta Kudu
Nov 30, 2018 12:23Majalisar dinkin duniya ta zargi reshen hukumar kula da 'yan gudun hijira a Afrika da yin amfani da kudaden hukumar ba ta hanyar da ta dace ba.
-
Al'ummar Zimbabwe Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Kasar
Nov 30, 2018 07:45Dubun dubatan al'ummar kasar Zimbabwe musamman masu adawa da gwamnatin kasar sun gudanar da wata zanga-zanga a babban birnin kasar, Harare don nuna rashin amincewarsu da matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar musamman karancin kayayyakin bukatun yau da kullum cikin har da man fetur.
-
Boko Haram : Kasashen Yankin Tafkin Chadi Sun Bukaci Taimakon Duniya
Nov 30, 2018 00:06Kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru, sun bukaci taimakon kasashen duniya a yakin da suke da kungiyar Boko Haram.
-
Za'a Fara Yi Wa Wasu Shugabannin 'Yan Awaren Kamaru Da Ake Zargi Da Ayyukan Ta'addanci Shari'a
Nov 29, 2018 14:17An sanar da ranar da za a fara yi wa wasu shugabannin 'yan awaren kasar Kamaru su 10 da aka dawo da su kasar daga Nijeriya shari'a bisa zargin gudanar da ayyukan ta'addanci wadanda ana iya yanke musu hukuncin kisa idan har aka same su da laifi.
-
Sudan Ta Musanta Batun Cewa Tana Gudanar Da Wata Tattaunawar Sirki Da 'Isra'ila'
Nov 29, 2018 14:16Gwamnatin kasar Sudan ta musanta wasu labarai da ke gwamnatin ta gudanar da wata tattaunawa ta sirri da haramtacciyar kasar Isra'ila a kasar Turkiyya.
-
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Ce Sojoji 23 Ne Aka Kashe A Harin Metele Ba 100 Da Wani Abu Ba
Nov 29, 2018 14:16Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewar sojoji 23 ne aka kashe a harin da 'yan Boko Haram suka kai wani sansanin sojojinta da ke gariin Metele na jihar Borno ranar 18 ga watan Nuwamba nan sabanin wasu rahotanni da suke cewa sama da sojoji 100 ne aka kashe yayin harin.
-
Gabon : Ali Bongo Ya Fara Jinya A Morocco
Nov 29, 2018 07:34Rahotanni daga Morocco na cewa Shugaba Ali Bongo Ondimba na Gabon ya isa birnin Rabah, da sanyin safiyar yau Alhamis, inda zai ci gaba da jinya, bayan da ya bar kasar Saudiyya inda ya kwashe sama da wata guda na jinya.